Rundunar sojin Nijeriya, za ta tura jirgin ta zuwa jihar Kwara domin sa ido a zaben gwamna da na majalisun jihohi da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kwara Kayode Egbetokun, ya ce an yanke shawarar ne domin tabbatar da cikakken tsaro a lokacin zaben.

Ya kuma bukaci al’umma kada su ji tsoro, su fito su halarci rumfunan zabe, ya na mai cewa za a tura jirgin sama domin kula da harkar zabe, maimakon jirgin ‘yan sanda da aka yi amfani da shi a zaben baya.

Shugaban rundunar sojin sama na jihar Kwara Air Commodor A. Adamu, ya ce za a yi amfani da jirgin soji ne saboda jirgin da aka yi amfani da shi a baya ya na daga cikin jiragen da aka tura yankin Arewa maso Gabas domin yakar ‘yan ta’adda.

A cewar shi, amfani da jirgi ya fi sauri da sauki, kuma zai taimaka cikin gaugawa a wuraren da ke fuskantar kalubale.