Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta jihar Rivers, ta ce ta tanadi jami’ai dubu 15 da 544 da za su taimaka wajen samar da tsaro a zaben gwamna da na majalisun jihohi da za ayi a ranar Asabar mai zuwa.
Wannan kuwa ya na zuwa ne, a lokacin da jam’iyyar PDP a jihar ke kira ga Hukumar Sojin Nijeriya ta saki kwamishinan Ilimi na jihar Dr Tamunosisi Gogo-Jaja da iyalan sa da kuma Benjamim Diri da aka kama a Fatakwal.
A jawabin da ya yi wa manema labarai a garin Fatakwal, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Rivers Usman Balel, ya ce akalla jami’ai dubu 1 da 500 daga sauran hukumomin tsaro aka tanada domin zaben da za a gudanar a jihar.
Ya ce za a takaita zirga-zirgar masu shige da fice daga karfe 12 na daren Juma’a zuwa karfe 6 na yammacin ranar Asabar, kuma za a rufe dukkan hanyoyin shiga jihar har zuwa bayan zabe.
Shugabanin
jam’iyyar PDP na jihar Rivers, sun ce sojoji sun yi awon gaba da kwamishinan
ilimi na jihar GogoJaja tare da iyalan sa, a lokacin da su ka yi kutse cikin gidan
sa da ke Fatakwal a yammacin ranar Larabar da ta gabata.