Alaranma Ahmad Sulaiman Ibrahim
Alaranma Ahmad Sulaiman Ibrahim

Fittacen malamin addinin Musulunci Alaramma Ahmed Suleiman, ya bayyana irin ukubar da su ka shiga a hannun masu satar mutane don kudin fansa.

An dai yi garkuwa da malamin ne a ranar 14 ga watan Maris a kan hanyar karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Da ya ke jawabi a fadar sarkin Katsina jim kadan bayan ceto shi, Malamin ya ce al’amarin mummuna abin tunawa ne.

Ya kara da cewa, a kullum ‘yan ta’addan su kan ce ma su tun da yanzu aka ce hukuma ta shiga to Malam ba za ku koma gida ba, ko kuwa an kawo kudin nan sai mun kashe ku.

Malamin ya kara da cewa, sai dai a dauki hakan a matsayin jarabawa kuma darasi ne, domin Allah ya kan jarraba bawa don ya daga darajar sa ko yafe masa wasu zunubbai.

Leave a Reply