Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDM Fasto Aminchi Habu, ya maka shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe kotun daukaka kara.

Fasto Habu dai ya shigar da korafin ne gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, bisa zargin rashin adalcin da ya ce an yi a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu.

A cikin bukatun da ya gabatar, Faston ya na neman kotun ta soke nasarar shugaba Buhari da jam’iyyar APC, tare da neman hukumar zabe ta kasa ta sake gudanar da wani sabon zaben kujerar shugaban kasa.

Korafin Fasto Habu, ya faru ne biyo bayan ikirarin rashin adalci da hukumar zabe ta yi masa na rashin sanya sunan sa da na jam’iyyar a cikin takardun zabe, wanda ya ce hakan ya yi sanadiyar haramta ma shi takara a zaben da ya gabata.

Dan takarar, ya bayyana bakin cikin sa game da yadda hukumar zabe ta zame masa ciwon ido, bayan ya batar da dimbin dukiya wajen gudanar da yakin neman zabe.

Leave a Reply