Yan kungiyar Boko Haram sun kai kari a garin Miringa da ke cikin karamar hukumar Biu ta jihar Borno, yayin da jama’a ke Sallar Magariba inda su ka rika harbe-harben manyan bindigogi.

Rahotanni sun ce yan ta’addan sun kai harin ne a barikin Soji, inda su ka kashe jami’in dan sanda daya da wani mutum daya.

Mayakan na Boko Haram, sun dira garin ne a cikin motoci 13, inda su ka kona barikin sojin tare da banka wa wata makarantar firamare wuta.

 Wani mazaunin garin mai suna Abba Usman, ya ce daga baya ne su ka koma muhallan su, inda su ka tarar an kona barikin sojin da masaukin sojin da mota da kuma wani sashen makarantar firamare.

Leave a Reply