Audu Ogbeh, Ministan Harkokin Noma
Audu Ogbeh, Ministan Harkokin Noma

Ministan harkokin noma Audu Ogbeh, ya ce masu shigo da kayayyaki daga kasashen ketare su ne manyan makiyan Nijeriaya kokarin da kasar ke yi na bunkasa amfani da kayayyakin cikin gida.

Audu Ogbeh ya bayyana haka ne a Abuja a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar zartaswa kan noma domin kare kasafin da aka warewa ma’aikatar sa.

Ya ce kayayyakin da ake shigowa da su Nijeriya irin su tsinke sakacen hakori da sukari da kayan lambu da Fensiri na matukar ciwa gwamnati tuwo a kwarya, a kokarin da na tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun sayi kayayyakin da aka sarrafa su a cikin gida.

Kawo yanzu dai, an fara aiki da wasu kamfanoni biyu, kuma ana sa ran nan da karshen wannan shekarar za a dakatar da masu shigo da tumaturin da aka sarrafa cikin Nijeriya.