Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya maida wa shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Ibrahim Magu martani a kan irin kudaden da aka sata a lokacin mulkin Jonathan.
Jonathan ya yi wannan martani ne ta bakin tsohon hadimin sa Reno Omokri, inda ya ja hankalin gwamnatin shugaba Buhari da ta ji da rahoton da kasar Amurka ta fitar a kan irin barnar da ake yi a Nijeriya.
Idan dai ba a manta ba, a kwanakin baya ne Amurka ta gano cewa, akwai alamar tambaya a game da yaki da satar da gwamnatin tayya ke yi, saboda haka a cewar Omokri, Ibrahim Magu ya daina batawa kan sa lokaci wajen yi wa Jonathan sharri.
Sai dai Ibrahim Magu ya bayyana cewa, an sace sama da Tiriliyan 1 a lokacin da Goodluck Jonathan ke mulki.
Omokri yace a shekara ta 2016 ne Lai Muhammad ya ce an yi awon gaba da Tiriliyan 1 da biliyan 3 daga 2006 zuwa 2013, haka kuma Farfesa Itse y ace gwamnatocin Obasanjo da ‘Yar adua da Jonathan sun saci Naira Tiriliyan 1 da biliyan 4 a shekaru 7.
A karshe Omokri ya bayyana irin badakalar da aka tafka a kamfanin NNPC kwanakin baya.