Alaranma Ahmad Sulaiman Ibrahim
Alaranma Ahmad Sulaiman Ibrahim

‘Yan bindigar da suka sace Alaranma Ahmad Sulaiman Ibrahim sun sako shi bayani ya kwashe kimanin kwamaki 13 a hannun su.

A Yau dinann 27 ga Watan Maris mu ka samu wannan labari na farin ciki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, sheikh Ahmad Sulaiman ya dawowa gida bayan wasu masu garkuwa da mutane sun sace sa kwanakin baya.

Malam Muhammad Kabir, shi ne wanda ya bayyana haka a madadin Iyalin alramman, inda ya kara da cewa yanzu Sheikh Ahmad Sulaiman ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

Idan dai ba a manta ba, masu garkuwa da mutane sun sace Ahmad Sulaiman Ibrahim da wasu malamai 5 a kan hanyar Sheme zuwa Kankara.

Leave a Reply