Majalisar wakilai ta gargadi Ministan harkokin jiragen sama Hadi Sirika a kan sabon shirin san a karbo bashin wasu makudan  kadade har Dala 461 domin yin wasu aikace-aikace.

‘Yan majalisar sun ce, Ministan na da niyyar karbo bashin kudi ne da sunan wasu gyare-gyare da za ayi a filin jiragen sama na Nijeriya.

Bayanin hakan dai na zuwa ne kwanakin kadan bayan Hadi Sirika ya karbo rancen Dala miliyan 500 da nufin aiki da su.

Shugaban kwamitin harkokin jiragen sama a majalisar ya ce, bayan wadannan tarin kudade, an warewa ma’aikatar kudi har Naira biliyan 47 da miliyan 5 a cikin kasafin kudin shekara ta 2019.