Kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari, ya zargi jam’iyyar PDP da satar hanya ta na’ura mai kwakwalwa domin leka bayanan sirrin hukumar zabe ta kasa.

Kakakin kwamitin Festus Keyamo ya bayyana haka, a cikin wata takardar korafi da ya aike wa shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS.

Bayanan da ke cikin na’urar dai su na daga cikin abubuwan da Atiku Abubakar ke kafa hujja da su a karar da ya shigar kotu.

Atiku Abubakar, ya ce bayanai daga na’urar sun nuna yadda aka rage ma shi kuri’u a zaben shugaban kasa na jihohi 31 da birnin tarayya Abuja.

A cikin karar da ya shigar, Atiku Abubakar ya ce ya kada shugaba Buhari da tazarar kuri’u miliyan 1 da dubu 615 da 302.

Ya ce na’urar ta nuna cewa, ya samu adadin kuri’u miliyan 18 da dubu 356 da 732, yayin da shugaba Buhari ya samu kuri’u miliyan 16 da dubu 741 da 430.

Atiku ya ce, bayanai sun tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaben kujerar shugaban kasa, amma hukumar zabe ta bayyana sunan shugaba Muhammadu Buhari.