Rahotanni na cewa an samu karancin fitowar masu zabe a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba, a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da aka a Asabar dinnan a Najeriya.

Tun da sanyin safiya ne dai jama’a suka soma fita zuwa rumfunan zabe a wasu wuraren, ko da yake a wasu rumfunan zaben an ce ba’a fito ba sosai.

Wasu masu kada kuriar da aka tattauna da su sun danganta lamarin na rashin fitowan da rashin cika alkawurran shugabanin dake kan mulki ke yi.

Ya zuwa yanzu babu wani rahoton tashin hankali a jihohin Adamawa da Taraba, yayin da aka fara hada sakamakon zaben.

Leave a Reply