Rahotanni sun ruwaito cewa, an fara zaman sauraron karar da Atiku ya shigar gaban kotun sauraron koken zaben shugaban kasa, inda ya zargi hukumar  INEC da jam’iyyar APC da shirya magudi wanda hakan ya ba Buhari nasarar lashe zaben.

Sai dai wasu rahotanni sun ruwaito cewa, tuni shugaban kasa Buhari ya kammala tara wasu tawagar lauyoyi da za su tsaya domin kare martabar nasarar da ya samu.

Jagoran tawagar lauyoyin su hada da Cif Wole Olanipekun, twanda sohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa sai kanin mataimakin shugaban kasa Akinola Osinbajo da kuma kakakin yakin neman zaben shugaba Buhari Festus Keyamo.

Sauran sun hada da tsohon shugaban kungiyar lauyoyi na kasa  Abubakar Mahmoud da Femi Atoyebi da Mike Igbokwe da Niyi Akintola da Yusuf Ali da Osaro Egbobamien da Dakta Muiz Banire da dai sauran su.

Wannan dai it ace tawaga mafi karfi da ka ta ba samu da zata jagoranci wata shari’a, wanda haka ta sa ake ganin ba za a taba tara kwarrru da gogaggu masana shari’ar kamar wannan ba.

Leave a Reply