Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama ‘yan bangar siyasa a kalla 100 tun daga lokacin fara yakin neman zabe zauwa yau.

Rundunar ta tabbatar da cewa, ba za ta kyale wasu suna tayar da hankalin jama’a ba, inda ta ce duk wanda bai shiga taitayin sa ba, zai shiga hanun ta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ali Janga ya tabbatar da haka lokaci wani taron manema labarai da ya gudana a Bauchi, inda ya ce rundunar sa ba zata kyale wasu ‘yan sara suka da ‘yan bangar siyasa su rika tada hankalin jama’an ba.

Janga ya ce, wadannan kamen sun yi ne gabanin gudanar da zaben shugaban kasa da aka gudanar makonni biyu da suka gabata, inda ya kara da cewa, ana zargin matasan da aikata laifukan da suka jibinci tayar da hankali da sara suka a fadin jihar.