Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama babban akawun kudi na gwamnatin jihar Imo Uzo Casmir bisa zargin sa da karkatar da wasu makudan kudaden jihar.

Haka kuma hukumar EFCC na zargin Casmir da hada kai da gwamnan jihar Imo wajen karkatar da kudaden jihar da su ka kai naira biliyan 1 da dubu hamsin domin siyen kuri’u a zaben gwamna da na ‘yan majalisun dokokin jihar.

Hukumar EFCC reshen jihar Enugu ta tabbatar da kamen, inda ta ce yanzu haka ta na gudanar da bincike a kan lamarin.

Leave a Reply