Shugaban kwamitin man fetur na majalisar dattawa Sanata Kabiru Marafa, ya rubuta takarda zuwa ga shugaban kotun daukakak kara ta Nijeriya game da rigimar jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

Marafa ya aika takardar ne zuwa ga mai shari’a, Zainab Adamu Bulkachuwa, ya na mai kokawa da bata lokacin da ake samu wajen nada mutanen da za su duba rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

Sanatan ya shaida wa mMai shari’a Zainab Bulkachuwa cewa, jinkirin da kotun ta ta ke yi wajen fitar da kwamitin da zai saurari kukan ‘yan jam’iyyar APC a jihar Zamfara, alamu ne da ke nuna za a yi masu rashin adalci a gaban shari’a.

Marafa ya rubuta wa shugabar kotun takardar ne tun ranar 13 ga Watan Maris tare da wasu mutane 142, inda ya tunawa kotun cewa akwai bukatar a duba lamarin APC na jihar kafin lokaci ya kure, domin lokacin da doka ta tanada don a dauki mataki a jam’iyyar ya na daf da kure masu.