Jami’iyyar PDP ta ce, kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ba zai sa baki a zabubbukan da za a maimaita a wasu jihohi ba sun tabbatar da cewa, ya yarda an tafka magudin zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

PDP ta ce, kalaman shugaba Buhari wani salo ne na janye hankalin jama’a daga magudin da jam’iyyar APC ke shiryawa a zaben da za a yi a jihohi 6 ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Jam’iyyar PDP ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran ta Kola Ologbondiyan ya fitar.

Ologbondiyan ya kara da cewa, kalaman shugaba Buhari da ke cewa wasu ‘yan Jam’iyyar  APC su na matsa ma sa lamba a kan ya sa baki domin a yiwa ‘yan takarar ta alfarma, ya isa jama’a su fahimci yadda jam’iyyar ta kware a bangaren tafka magudin zabe.

Jam’iyyar PDP, ta yi kira ga dakarun soji su nesanta kan su daga wuraren zabe tare da jan hankalin hukumar zabe ta kasa ta tabbatar ta ba jama’a abin da su ka zaba musamman a jihohin da PDP ta ba APC tazarar kuri’u.