Hukumar Tsaro rundunar Sojin Nijeriya, ta ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC ta watsa mata kasa ido tare da kwance mata zane a kasuwa.
Rundunar ta yi wannan bayani ne, bayan hukumar zabe ta zargi sojoji da ‘yan jagaliyar siyasa da laifin hargitsa zaben gwamna a jihar Rivers.
Hargitsin da ya faru ne ya tilasta hukumar zaben dakatar da ci-gaba da tattara sakamako da kuma bayyana sakamakon zaben.
Kakakin Rundunar Sojin Bataliya ta 6 da ke Fatakwal Aminu Iliyasu, ya ce sojoji sun yi nadama da jin haushin yadda hukumar zabe ba ta sanya bayanan da sojoji su ka gabatar wa Kwamitin Binciken da ta gabatar a Fatakwal ba.
Ya ce wannan ya nuna rashin gaskatawar da hukumar zabe ta yi wa sojojin Nijeriya, wadanda su ka sadaukar da kan su domin ganin hukumar ta gudanar da aikin ta yadda ya dace.
Haka kuma, sojoji sun ce sun yi mamakin ganin yadda hukumar zabe ba ta sanya rahoton da aka kashe wasu sojoji biyu ta hanyar yi masu mummunan kisa ba.