Janar Tukur Buratai, Shugaban Rundunar Sojin Kasa
Janar Tukur Buratai, Shugaban Rundunar Sojin Kasa

Shugaban Rundunar sojin Nijeriya Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ce labarun karya ne su ke haddasa yawan rikice-rikicen zabe a fadin kasar nan.

Da ya ke jawabi    yayin kaddamar da sabbin ayyuka a sansanin soji da aka sanya wa suna sansanin Buratai a jihar Bayelsa, Buaratai ya ce yada labarun karya ne su ke kashe tsarin damokradiyya da ayyukan soji.

Janar Tukur Buratai, wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Adamu Saliu, ya ce ya kaddamar da aikin Operation Safe Conduct kafin zaben shekara ta 2019, domin tabbatar da nasara a zaben.

Buratai ya kara da cewa, ya kuma kaddamar da dakin tattara bayanai na soji domin lura da al’amurran zabe ciki har da magance yada labarun karya.

Ya ce yan ta’adda da masu tada kayar baya su na amfani da shafukan sada zumunta na zamani, domin yada labarun karya da gangan don su haifar da rudani da kuma barkewar rikici.8e���|

Leave a Reply