Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta bayyana dalilin da ya sa ta hana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar duba kayayyakin zabe.
Atiku Abubakar dai ya garzaya kotu ne bayan ya fadi a zaben ranar 23 ga watan Febrairu, domin kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari.
Idan dai ba a manta ba, a cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP ya fitar, ya ce hukumar zabe ta ki bin umurnin kotu kuma ta hana Atiku Abubakar duba kayayyakin da aka yi amfani da su.
Sai dai daraktan yada labarai na hukumar zabe Oluwole Osaze-Uzzi ya karyata maganar, yayin da ya yi wa manema labarai bayani, inda ya ce ba gaskiya ba ne cewa an hana jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar duba kayayyakin zabe.
Ya ce ba su samu takardar bukatar su ba sai ranar Juma’ar da ta gabata, kuma a shirye su ke su ba su abin da su ke so a duk lokacin da su ka shirya. 0