Gwamnan jihar Mohammed Abubakar, ya kai karar hukumar Zabe wajen shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Mohammed Abubakar, ya ce ya garzaya fadar shugaban kasa ne domin ya yi wa shugaba Buhari cikakken bayani game halin da jihar Bauchi ta ke ciki dangane da zaben gwamna da aka yi da matakin da humar zabe ta dauka.
Ya ce matakin da hukumar zaben ta dauka ya saba wa dokar kasa, domin doka ta ce muddin aka sanar da sakamakon zabe babu dalilin sake dawo da maganar baya.
Da ya ke zantawa da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Gwamna Abubakar ya ce, ya garzayo domin ya sanar da shugaba Buhari halin da ake ciki a jihar Bauchi.
Ya
ce abin da hukumar Zabe ta yi ya saba wa doka, domin ta riga ta bayyana
sakamakon zabe da kuma wuraren da zabe bai kammalu ba, don haka babu yadda za a
wayi gari a ce an jingine wancan hukunci sai an sake kirga kuri’u.