Jami’an tsaro sun ce sun kama wasu ‘yan sanda shida, dangane da cinna wa ofishin Rajistar masu zabe wuta da wasu batagari su ka yi a Jihar Ebonyi.

Wadanda aka kama dai an tura su ne domin kula da kayan zabe a ofishin da ke Karamar Hukumar Ezza ta Arewa a Jihar Ebonyi.

Wasu batagari sun kai wa ofishin hari ne da misalign karfe biyu na dare a ranar zabe su ka kone ofisoshi uku kurmus.

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa ta ce, ofishoshin da aka boye kayan zabe masu matukar muhimmancin ne aka kone.

Rahotanni sun ce an kama jami’an tsaron shida ne, saboda sun kyale batagarin matasan har su ka samu kafar kone ofisoshin.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Awoshola Awotinde ne ya badar umurnin kama jami’an, bayan ya gabatar da mataimakin shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya na Shiyyar.

Kakakin Yada Labarai ta rundunar ‘yan Sanda ta jihar Ebonyi Loveth Odah, ta tabbatar da kama yan ’yan sandan shida, ta na mai cewa kona kayan zaben ya haifar da tsaikon jefa kuri’a ga jama’a sama da 36,000, lamarin da ya sa aka ce zaben bai kammalu ba.

Leave a Reply