Gwamnatin Tarayya Ta Ce Ta Kammala Dukkan Shirye-Shirye Don Sayar Da Dam Guda Shida Ga ‘Yan Kasuwa Masu Zaman Kansu Da Kuma Mayar Da Shirin Ta Na Banki Raya Masana’antu.

Ministan Ayyukan Lantarki Da Gidaje, Babatunde Fashola Ya Sanar Da Hakan A Lokacin Taro Karo Na 29 Na Masu Ruwa Da Tsaki A Fannin Wutar Lantarki Da Aka Gudanar Minna Cikin Jahar Neja.

Ya Ce, Manufar Ita Ce Ba Cibiyoyin Ilimi Da ‘Yan Kasuwa Dama.

Fashola Ya Kara Da Cewa, Wannan Duk Tsarin Gwamnati Ne Akan Kudurin Ta Na Kara Samar Da Wuta A Karkara Da Shugaban Kasa Ya Amince Da Hakan A 2016.

A Bangaren Wutar Lantarki, Fashola Ya Kara Jaddada Cewar, Kamfanonin Samar Da Wutar Sune Ke Kawo Cikas Akan Samar Da Wutar A Nigeria.  

A Karshe Ya Yi Nuni Da Cewar, Manyan Kalubale A Tsarin Samar Da Iskar Gas Sun Hada Da, Yadda Za A Samara Dashi Da Tura Shi Ganin Cewar A Yankin Akwai Megawatts Data Kai Yawan 2,000.

Leave a Reply