Kungiyar Tuntuba Ta Arewa Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Ci Gaba Da Binciken Yiwuwar Samun Albarkatun Man Fetur Har Sai An Cimma Gaci A Arewa.

Shugaban Kungiyar Kwamitin Amintattu Na Kungiyar Adamu  Fika, Ya Bayyana Haka A Lokacin Da Ya Jagoranci Tawagar ‘Ya’yan Kungiyar Zuwa Ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Fika Ya Tunatar Da Shugaban Irin Rokon Da Kungiyar Ta Masa A Baya Kan Aikin Tashan Jiragen Ruwa Na Kan Tudu Na Baro, Da Kuma Aikin Samar Da Wutar Lantarki Na Mambila.

Ya Kara Da Cewa Baya Ga Wannan Kungiyar Ta Shawarci Shugaba Buhari A Baya Kan Inganta Harkokin Aikin Noma, Gyaran Hanyoyi, Aikin Neman Albarkatun Man Fetur Da Sauran Su.

Fika Ya Ce A Shekarar 2016, Kungiyar Karkashin Jagorancin Marigayi Yusuf Maitama Sule, Ta Jawo Hankalin Gwamnatin Tarayya Kan Ayyuka Da Za Su Kawo Ci Gaban Kasa.

 Ya Ce Abin A Yaba Ne Duba Da Cewa Kawo Yanzu An Kammala Aikin Madatsar Wutar Lantarki Ta Mambila Da Kuma Tashar Jiragen Ruwa Ta Baro, Gashi Kuma An Maida Hankali Akan Sauran Ayyuka.