Hukumar Wayar Da Kan Al’umma Ta Kasa Noa Ta Fara Wayar Da Kan Masu Kada Kuri’a A Jihohi 7 Dake Shiyoyin Siyasar Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Babban Daraktan Hukumar Garba Abari, Ya Jagoranci Taron Kwanaki 2 Da Hukumar Ta Shiryawa Al’ummomi, Kungiyoyi Da Masu Ruwa Da Tsaki Kan Ilimin Zabe A Kaduna.

Abari Wanda Ya Samu Wakilcin Daraktan Aikace-Aikace Na Hukumar David Akeji, Ya Ce Makasudin Shirya Taron Shine Domin Tabbatar Da Cewa Masu Ruwa Da Tsaki Sun Mallaki Ilimin Da Ya Kamata Su Samu Kan Harkokin Zabe.

Ya Ce Akwai Jam’iyyu Daban-Daban Wadanda Tambarin Su Ya Kusa Zuwa Irin Guda, Akwai Kuma Wadanda Sunayen Su Ne Ka Kamancecenya Da Juna, Wanda Idan Ba Da Wayar Da Kan Al’umma Ba Za A Rika Samun Matsaloli A Lokacin Zabe.

A Nata Bangaren Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Ce Shirya Irin Wadannan Tarurruka Zai Taimaka Wajen Banbancewa Tsakanin Jam’iyyun Siyasa A Lokacin Zabe.