Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bayyana tattara sama da shaidu 400 da zai yi amfani da su a kotun sauraron kararrakin zabe, domin kalubalantar sakamakon zaben da shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.

Mai ba jam’iyyar PDP shawar a kan harkokin shari’a Emmanuel Enoidem ya bayyana haka, yayin ganawa da manema labarai a harabar kotun daukaka kara da ke Abuja.

Mista Enoidem ya kara da cewa, manyan lauyoyi masu lambar girmamawa ta SAN guda 20 ne za su tsaya wa Atiku Abubakar.