Rahottani sun tabbatar da cewa, Boko Haram sun kai wani hari tare da kokarin shiga garin Michika da ke jihar Adamawa da karfin tuwo.
Sai dai rahotaanni sun ce, mayakan sun hadu da jajirtattun sojojin da suka tare su aka yi gumurzu, inda aka kwashe tsawon sa’o’i ana barin-wuta a tsakanin bangarorin biyu.
Wasu mazauna garin Michika sun shaida wa manema labarai cewa, sun fara jin karar manyan bindigogi ne tun da misalign karfe 7 na dare a kan hanyar Michika zuwa Lassa, yayin da mayakan Boko Haram su ka yi yunkurin shiga garin na Michika.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Adamawa Ahmad Sajoh ya tabbatar da harin, inda ya ce mayakan Boko Haram sun yi kokarin shiga Michika ne bayan sun bi ta kauyen Kirchinga da ke kusa da Karamar Hukumar Madagali.
Sai dai ya ce kafin sojojin su kore su, sai da su ka kone Bankin First Bank tare da banka wa wasu shaguna wuta.