Wata babbar Kotu da ke Abuja, ta dakatar da hukumar zabe ci-gaba da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa domin bayyana wanda ya samu nasara a zaben Gwamnan Jihar Bauchi.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya bada umurnin dakatar da shirin bayyana sakamakon, saboda bukatar hakan da lauyan gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar ya gabatar.

Tun farko dai Hukumar zabe ta bayyana cewa, sai an sake gudanar da zaben karamar hukumar Tafawa Balewa kafin sanin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi, amma daga bisani ta ce za ta sake tattara sakamakon zaben daga unguwanni zuwa karamar hukuma domin sanar da sakamakon. Alkalin kotun ya kuma bada umurnin ci-gaba da shari’ar cikin gaugawa, inda ya bukaci masu kara da lauyoyin hukumar zabe su gurfana a gaban sa ranar Larabar nan.