Hukumar yaki da almundahana da al’amurran zamba ICPC, ta yunkura domin kwace wasu kadarori mallakar Gidauniyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.
Hakan kuwa, ya biyo bayan zargin Gidauniyar da aka yi da laifin karya ka’idojin mallakar filaye ko kadarori da ke cikin dokokin Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar ICPC Rasheedat Okoduwa ta fitar, ta ce ICPC za ta kwace kadarorin ne nan ba da dadewa ba.
Sai dai ta ce kwace kadarorin da za a yi na wucin-gadi ne, amma daga bisani za ta garzaya kotu domin a ba ta iznin karbe kadarorin na dindindin.
Hukumar ICPC ta ce, kadarorin da za ta kwace su na wurare daban-daban ne a birnin Abuja, kuma yawan kudin su ya kai jimillar naira biliyan 4 da miliyan 8.
Daga
cikin kadarorin da za kwace kuwa akwai wani makeken fili da ba a yi gini a
cikin sa ba, da gida, da wata katafariyar gona ta Maidubu Farm and Construction
Limited da sauran su.