Majalisar wakilai ta dage zaman ta zuwa ranar 2 ga watan Afrilu, domin ta ba ‘yan majalisar damar zantawa da hukumomi a matakin kwamiti dangane da gabatar da tsarin kasafin shekara ta 2019.
Hakan kuwa, ya biyo bayan shawarar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya gabatar a zauren majalisar.
Da ya ke zartar da hukunci, mataimakin shugaban majalisar Yussuf Lassun, ya bukaci dukkan kwamitocin majalisar su yi aiki, sannan su kammala muhawara a kan kasafin kafin watan Mayu.
Yussuf
Lassun, ya ce dokar kasafin ta kammalu domin gabatar da shi da zarar sun koma
majalisar a watan Mayu.