Yaki da halasta kuddaden haram, da kuma daukar nauyin ayukan ta’addanci da ke ci gaba da wahalar da kasashe da dama a yankunan dake amfani da kuddaden bai daya na Cfa ne, babban makasudin zaman taron ministocin kudin kasashen yankin da aka fara a jiya alhamis a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer, da zai taimaka don kawo karshen lamarin.

Manazarta dake halartar wannan taro a Nijar sun bayyana cewa muddin Shugabanin kasashen yankin suka kasa samar da hanyoyin da suka dace wajen dakile kwarrarar mayakan dake samun goyon bayan wasu manyan kasashen Duniya, za a fuskanci matsala.

Rahoton na masana zai taimaka zuwa kasashen Afrika don tanttance wasu daga cikin manufofin da za su taimaka cikin dan karamin lokacin don kawo karshen haka a yankin.

Leave a Reply