Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, Muhammad Babandede, ya karbi bakuncin takwarar sa na Ghana, Kwame Asuah Takyi, domin sulhunta batun korar wasu ‘Yan Ghana da Nijeriya ta yi a makon da ya gabata.

Takyi, ya ziyarci Shugaban hukumar NIS ne tare da rakiyar Jakadan Ghana a Nijeriya, Rashid Bawa.

A yayin ziyarar ta neman sulhu, shugabannin sun yi taron sirri a ranar Juma’ar da ta gabata, Sai dai, har zuwa lokacin rubuta wannan labarin babu wani karin haske kan abubuwan da aka tattauna.

Da aka tambaye shi, Babandede ya tabbatar da tattaunawar ta su, kana ya ce ana shirya abubuwan da za a kara tattaunawa a kai a tsakanin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Nijeriya da Ma’aikatar Harkokin Waje ta Ghana.

A makon da ya gabata ne dai, Nijeriya ta tasa keyar wasu ‘yan Ghana su hudu zuwa kasar su.

Leave a Reply