Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama wani malamin makarantar sakandare da ake zargi da tilastawa daliban makarantar da yake koyarwa yin lalata da su.
Ana zargin malamin da yin lalata da dalibarsa ‘yar shekara 18 domin kara mata maki, bayan ta fadi jarrabawar da ta rubuta.
Mai magana da yawun rundunar a jihar Legas, Bala Elkanah ya tabbatar da kama malamin da ake zargi da sakawa dalibar ‘yar shekara 18 da makin jarrabawa, bayan ya tilasta ma ta yin lalata shi da bakinta.
To sai dai kafin wannan ana zargin cewa malamin ya sha tilatawa wasu daliban yin wannan dabi’a.
An dade ana zargin wasu daga malaman sikandaren ‘yan mata da cewa suna yin lalata da dalibansu domin su ba su maki, ko kuma domin kara musu makin.
Lamarin ya sa har wata kungiyar dake yaki da tilasta yin lalata da mata ta yunkuro domin tabbatar da ma’aikatar ilimi a jihar Legas da kuma rundunar ‘yan sanda a jihar gudanar da bincike domin bankado gaskiyar lamri da ake zargin malamin da shi.



































