Gwamnatin tarayya ta ce za ta tabbatar da bin hanyoyin da suka kamata wajen gina tashar jiragen ruwa na kan tudu a garin Ibadan.

Ministan Sufuri, ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara Olorisa-Oko da Moniya dake Ibadan.

Ministan wanda ya samu rakiyar babban sakataren kungiyar masu jiragen ruwa ta Najeriya Hassan Bello, sun samu tarbar mataimakin gwamnan jihar Oyo Moses Adeyemo.

Ya ce hukumar ba za ta yi gaggawa ba wajen gudanar da aikin, amma zata tabbatar da cewa an bi hanyoyin da suka kamata wajen kammala aikin.

Ministan ya kuma yi alkawarin cewa nan bada jimawa ba za a fara gudanar da ayyuka a wuraren domin kammalawa cikin lokaci.

Ya kara da cewa da zarar an kammala aikin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi tare da rage zaman kashe wando a tsakanin al’umma da kuma inganta bangarori da dama a Najeriya.

Leave a Reply