President Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci masu zuba jari da su zuba jari a bangarorin bincike tare da ci gaba na jami’o’i dake fadin Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a wajen bikin yayen dalibai karo na 32 na shekarar 2018 zuwa 2019 a jami’ar Fatakwal, dake jihar Rivers.

Ya ce gwamnatin tarayya kadai ba za ta iya cimma dukkanin muradun jami’o’in gwamnati ba, a don haka akwai bukatar hadin gwiwar bangarori masu zaman kansu.

Shugaba Buhari, ya ce adon haka akwai bukatar karawa bangarori masu zaman kansu kwarin gwiwa wajen zuba jari a bangarorin bincike na jami’o’i.

Buhari, wanda ya samu wakilcin karamin ministan Ilimi Anthony Onwuka, ya ce an samu ci gaba sosai a bangaren jami’o’i, a shekarun 4 da suka gabata.

A cewarsa gwamnatin tarayya ta fitar da kudade na sake gina sabbin tsare-tsare, da sayen kayayyakin aiki, tare da ware kudade gas ashen bincike na jami’o’i.

Leave a Reply