An kammala tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jama’an kasashen Sin da Amurka karo na 8 a birnin Beijing a na Sin Watau China.

An shafe kwanaki biyu ana tattaunawar wadda ke karkashin jagorancin jami’in hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firayin ministan kasar kuma jagoran bangaren kasar Sin kan tattaunawar tattalin arziki dake tsakaninta da Amurka wato Liu He, da wakilin cinikayyar Amurka Robert Lighthizer da ministan kudin kasar Steven Mnuchin, inda sassan biyu suka tattauna kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar da za su daddale, haka kuma sun samu sabon ci gaba a kai.

A cikin watanni hudun da suka gabata, an yi tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jama’an kasashen Sin da Amurka har sau hudu, yanzu haka an shiga mataki mafi muhimmanci ke nan.

A cikin tattaunawar karo na 7 da sassan biyu suka yi, sun yi shawarwari kan batutuwan da suka shafi sayayyar fasahohi, da kare ikon mallakar fasaha, da matakan da za a dauka domin kayyade shigo da kayayyaki daga ketare da ba na karbar harajin kwastam ba, da aikin samar da hidima, da aikin gona da farashin kudin musaya da sauran su, sun kuma samu babban cigaba.

Leave a Reply