Hukumomin kasar Chadi sun ce yanzu haka dakarun su 500 suka kutsa kai cikin Najeriya domin taimakawa kasar yaki da mayakan kungiyar Boko haram.

Mai Magana da yawun rundunar sojin Chadi, ya ce sojojin na daga cikin wadanda ke aiki a karkashin rundunar hadin kai da ta kunshi sojojin Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar.

Rahotanni sun ce akalla mutane sama da 200 suka mutu a cikin wannan wata sakamakon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai.