Mazauna wasu sassan garin Maidugri da ke jihar Borno, sun wayi gari da jin karar fashewar wasu abubuwa a wasu sassan garin, da suka hada da sansanin ‘yan gudun hijira na Teachers Village, da Bolori da kuma Pompomari.

Sai dai rahotanni sun rawaito cewa ba a samu hasarar rayuka ba, kasancewa abubuwan da suka fashe basu ritsa da kowa ba.

Fashewar abubuwan, ya zo ne bayan da wasu gungun ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton cewa mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kai farmaki garin Zabarmari, da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno a ranar Juma’a.

Rahotannin sun cigaba da cewa soji sun yi gaggawar maida martani, inda suka yi nasarar korar ‘yan ta’addan.

Sai dai mutane da dama sun tsere daga gidajen su, zuwa Maiduguri, kuma babu wani bayani, kan rasa rai.

Leave a Reply