Rahotanni daga Bauchi, sun ce wani gungun masu dauke da makamai sun sace jami’an hukumar zabe 4 a jihar.

Lamarin dai ya auku ne a wata rumfar zabe da ke karamar hukumar Jam’are, inda wani jami’in hukumar zaben da ya tsira, ya ce gungun mutanen sun zo ne cikin motoci kirar hilux 7, inda suka tarkata jami’an na INEC hudu da sauran kayan zabe sukai awon gaba da su.

Har yanzun dai babu wani karin bayani daga gwamnatin jihar ko kuma hukumar ‘yan sanda kan faruwar al’amarin.

A Jihar Sokoto inda nan ma aka gudanar da karashen zaben na Gwamna, wakilinmu ya rawaito cewa mutane da dama sun kada kuri’a cikin kwanciyar hankali, sai dai fa an samu hargitsi a wasu sassan jihar, ciki har da rumfar zaben Sarkin Adar Kwanni da ke cikin gari, da cikin garin Kedde, amma daga bisani jami’an tsaro suka shawo kan lamarin.

A Filato, kwamishinan ‘yan sandan Jihar Isaac Akinmoyode, ya shaidawa manema labarai cewa karashen zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, kazalika wakilinmu a jihar ya tabbatar da cewa ba’a fuskanci tashin hankali ba.

A jihar Bayelsa kuwa, hukumar INEC ta dakatar da kada kuri’a a mazaba guda daga cikin uku da karashen zaben na gwamna ya gudana, sakamakon umarnin yin hakan da kotu ta bada.

Shugaban hukumar zaben a jihar ta Bayelsa, Monday Udoh, ya ce umarnin ya shafi mazabar Brass ce ta daya, amma a sauran mazabun da suka hada da Ogbia ta 2 da Southern Ijaw komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.