Fadar shugaban kasa ta ce rade-radin da ake na cewa gwamnatin tarayya ta tsaida shirin Trader Moni ba gaskiya bane.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya yi wannan bayani ta bakin mai Magana da yawun sa Laolu Akande .

Mataimakin shugaban kasan, ya ce har gobe shirin Trader Moni, na aiki kuma zai cigaba har illa masha Allahu.

A wata sanarwa da Laolu Akande ya fitar a madadin ofishin mataimakin shugaban kasar, ya ce har gobe shirin Trader Moni na aiki kuma an samu kananan ‘yan kasuwa har su dubu 30, da aka rabawa jari bayan an kammala zaben ranar 23 ga watan fabreru.

Akande, ya ce an raba wa mutane da dama karin jari na Naira dubu 15 kowannen su domin su inganta harkokin kasuwancin su.

Ya ce kusan mutane dubu 30, da aka rabawa wannan kudi bayan zabe, a wannan karo sun fito ne daga jihohi 10.