Kungiyar tsofaffin tsagerun Neja Delta, ta yaba wa alheri da kuma kwazon gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari sakamakon biyan albashin su a kan kari.

Jagoran kungiyar ta masu tada kayar baya a yankin Neja Delta Godstime Ogidigba ne ya yi wannan yabo a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Benin na jihar Edo.

Ogidigba, ya ce kungiyar ta yanke shawarar bada lambar yabo a kan nagartaccen jagorancin babban mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin Neja Delta Farfesa Charles Dokubo.

Ya ce kungiyar ta yaba wa kwazon gwamnatin shugaba Buhari da Farfesa Dokubo, sakamakon biyan albashin tsofaffin tsagerun Neja Delta na kowane wata a kan kari, da kuma bada tallafin musamman ga matasan su domin dakile zaman kashe wando.

Ya ce yayin da gwamnatin shugaba Buhari ta shimfida shirin afuwa ga tsofaffin tsagerun Neja Delta da su ka ajiye makamai, a halin yanzu kungiyar su na ci-gaba da cin moriyar gwamnatin, biyo bayan sulhun da ke tsakanin su.

Leave a Reply