Wata kotun daukaka kara da ke jihar Sokoto, ta soke hukuncin wata babbar kotu da ta ba jam’iyyar APC damar tsaida ‘yan takara a jihar Zamfara.

Alkalan da su ka jagoranci zaman sauraren shari’ar sun ce, babbar kotun ta jihar Zamfara da ta ba jam’iyyar APC dama, ba ta yi nazari a kan hujjojin da aka gabatar mata kamar yadda ya kamata ba.

Bangaren Sanata Kabiru Marafa da su ka shigar da karar, sun bayyana farin ciki game da wannan nasara, sai dai lauyan da ya kare bangaren Gwamna Abdul-Aziz Yari ya ce za su yi nazari a kan hukuncin. A zaman kotun daukaka karar a birnin Sokoto, alkalan kotun uku a karkashin jagorancin mai Shari’a Tom Yakubu sun soke hukuncin babbar kotun ta jihar Zamfara.