Jigon jam’iyyar APC a jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, da dan takarar gwamna na jam’iyyar Ahmed Aliyu, sun musanta jita-jitar da ke cewa sun kira Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a kan zaben da aka yi ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Jawabin dai, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar APC Muhammadu Dingyadi ya raba wa manema labarai a Sokoto.

A baya dai wasu rahotanni su, ce Ahmed Aliyu da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sun kira Tambuwal na jam’iyyar PDP domin taya shi murnar samun nasarar lashe zabe.

An dai fitar da rahotannin ne, bayan hukumar zabe ta kasa ta bayyana Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben da tazarar kuri’u 342.

Leave a Reply