Kotun Da’ar Ma’aikata ta yi fatali da bukatar da dakataccen Alkalin Alkalai Walter Onnoghen ya shigar game shari’ar da ake yi ma shi a kan rashin bayyana wasu kadarorin sa.
Shugaban kotun Danladi Umar, ya ce dole Onnoghen ya gurfana a gaban kotun ya kare kan sa a ranar 1 ga watan Afrilu na shekara ta 2019.
A baya dai Onnoghen ya zargi kotun da rashin bin ka’ida wajen shigar da karar tuhumar sa da rashin bayyana wasu kadarorin sa.
Lauyan wanda ake kara Adegboyega Awomolo, ya ce an saba wa doka a wajen binciken Onnoghen gabanin shigar da karar kotu.
Walter Onnoghen, ya ce akwai kura-kurai da yawa a cikin karar da aka shigar a kan sa, inda ya ce ba su da masaniya a kan kadarorin sa da ya bayyana.
Ya ce zargin da ake yi masa duk tatsuniya ce da ba za a amince da ita a kotu ba, don haka ya nemi a yi watsi da karar._in_۴.D�l



































