Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ki rattaba hannu a kan wasu dokoki biyar da majalisar tarayya ta aike masa domin tabbatar da su a cikin dokokin kasa.
A cikin wasu wasiku daban-daban da ya aike wa shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, Buhari ya lissafa dokoki 5 da ya ki rattaba wa hannu, wadanda su ka hada da dokar cibiyar kula da basussuka ta kasa.
Sauran sun hada da dokar bunkasa hukumar kanana da matsakaitun masana’antu, da dokar gidauniyar kammala hada kamfanin Tama da Karafa na Ajaokuta, da dokar gidauniyar samar da gidaje a Nijeriya, da kuma dokar bankin rance na gwamnatin tarayya. Rahotanni sun tabbatar da cewa, adadin dokokin da shugaba Muhammadu Buhari ya ki rattaba wa hannu a majalisar tarayya ta 8 sun kai 31.





































