Kwanaki kadan kafin zabubbukan gwamnoni da ‘yan
majalisun dokoki na jiha, yanzu haka an fara samun zafafan
kalamai daga wassu jama’a, wanda idan ba a dakile su ba za
su iya janyo tashin hankali a tsakanin al’umma.

Daya daga cikin ababen da ke saurin harzuka jama’a,
musamman mabiya addinai shi ne furta kalamai game da
addini, wanda shi ne wasu ‘yan siyasa ke amfani da shi domin
rarraba kan jama’a da zummar cimma burin su.

Jihar Nasarawa dake da tarihin zaman lafiya tsakanin mabiya
addinai, a wannan karon an fara samun cece-kucen da ke rura
wutar rikicin da in ba a shawo kan shi ba zai iya zama
matsala.

Shugaban kungiyar hadin kan Kiristoci na Jihar Nasarawa
Rabaren Fada Sunday Emma, ya ce ba su bukatar wani
yanayin da zai bata zamantakewar su, yayin da sakataren
kungiyar Jama’atu na Jahar Nasarawa Imam Muhammad Ali
ya ce su na kan fadakarwa a kan zaman lafiya.

A shekarun baya dai irin wadannan kalamai marasa dadi sun
haddasa mummunan rikicin bayan zabe, wanda ya kai ga rasa
rayukan jama’a da salwantar dukiyoyi masu tarin yawa.