Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya aike wa Shugaba
Buhari wasikar musamman, ya na rokon ya gaggauta sa a
kama dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC Sadique
Abubakar bisa zargin ya na kokarin tada hankalin jama’a a
jihar.

Bala Muhammad, ya ce tunda aka fara yakin neman zabe,
Sadique Abubakar ya ke yin abin da yaga dama, inda ya ke
yawo da dakarun jami’an tsaro ya na tsorata al’ummar jihar
Bauchi.

Ya ce Sadiq Abubakar ya na tafiya ne da ayarin jami’an tsaro
dauke da makamai, da ‘yan barandar da aka dauko daga wajen
jihar domin ta’addancin adawar siyasa, lamarin da ya ce ya yi
sanadin mutuwar sama da mutane 3 da ba su ji ba ba su gani
ba, baya ga jikkata wasu da dama na kananan hukumomin da
ya ziyarta.

A karshe gwamna Bala Muhammad, ya yi kira ga shugaba
Buhari ya sa a kama Sadique Abubakar a kuma tsare shi.