The Nigerian Army has confirmed the case of a soldier who shot his colleagues and himself dead at Forward Operations Base, Rabah, Sokoto State.

Rundunar Sojin Nijeriya, ta fara bincike a kan wani soja bisa
zargin harbe abokan aikin sa, sannan ya kashe kan sa a
sansanin sojoji da ke Rabbah a Jihar Sokoto.

Kakakin rundunar Birigediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya
ce ya zuwa yanzu ba a tantance hakikanin abin da ya faru ba,
amma sojan ya harbe kan sa bayan ya hallaka abokin aikin sa.

Nwachukwu ya kara da cewa, Babban Hafsan Runduna ta 8
kuma Kwamandan hundunar haɗin gwiwa ta Hadarin Daji
Manjo Janar Godwin Mutkut da wasu manyan hafsoshi sun
ziyarci wajen da lamarin ya faru.

Ya ce GOC ya jajenta wa sojojin da su ka rasa abokan aikin
su a sansanin, sannan ya bukaci su zama masu kula da junan
su, sannan su bada rahoton duk wani rikici da ke faruwa a
tsakanin su domin gudun sake faruwar irin haka.