Kungiyoyin kare hakkin bil Adama, sun yi kira ga
hukumomin Nijeriya su kawo karshen hare-haren da ke
salwantar da rayukan al’uma.

Kiran dai ya na zuwa ne, bayan wasu hare-haren da su ka yi
sanadiyyar mutuwar mutane 35 a jihohin Katsina da Kaduna a
karshen makon da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Amnesty
International ta nemi hukumomin Nijeriya da su dauki
matakan gaugawa domin kawo karshen hare-haren ‘yan
bindiga a kudancin jihar Kaduna.

Kungiyar ta Amnesty, ta ce an kashe akalla mutane 366
tsakanin watannin Janairu da Yuli na shekara ta 2020, ta na
mai cewa hukumomi su na nuna gazawa wajen hukunta
wadanda ke kitsa wadannan hare-hare.