Fadar shugaban kasa ta zargi jam’iyyar PDP da kokarin lalata tsarin demokradiyar Nijeriya tun bayan da ta sha kaye a zabubbukan da su ka gabata.

Wannan jawabin dai ya na zuwa ne, yayin da jam’iyyar PDP ke zargin jam’iyyar APC da shirin tada hankula a jihar Taraba saboda a zartar da dokar ta baci kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

PDP kuma ta yi ikirarin cewa, jam’iyyar APC ta na shirin tafka magudi a zaben jihar Sokoto ta hanyar amfani da sojoji domin razana masu zabe.

Yayin da ya ke maida martani a kan zargin, mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu, ya ce radadin shan kaye ne ya sa PDP ke furta irin wadannan kalamai.

Leave a Reply