Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce babu dalilin da zai sa jam’iyyar APC ta yi sanyin jiki ko jan-kafa wajen tabbatar da ganin ta lashe zabubbukan da za a maimata a wasu jihohi ranar 23 Ga Maris.
A dukkan jihohin da za maimaita zabubbukan dai jam’iyyar PDP ce kan gaba in ban da jihar Filato.
Osinbajo ya yi wannan furuci ne, yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar yakin neman zaben Buhari da Osinbajo da aka shirya wa walimar cin abinci a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Farfesa Yemi Osinbajo, ya gode masu dangane da rawar da su ka taka wajen sake zaben jam’iyyar APC ta cigaba da mulki a Nijeriya.
Ya
ce a wannan zango na biyu, tattalin arziki zai bunkasa ta yadda Nijeriya za ta
zama kasaitacciyar kasa.